logo

HAUSA

NDLEA ta kwace kilogram 13 da hotar iblis a filin jirgin saman Najeriya

2022-04-11 10:22:47 CMG Hausa

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta sanar cewa, ta kwace kilogram 13.2 na hotar koken a filin jirgin saman kasa da kasa na Murtala Muhammed a birnin Legas, cibiyar kasuwancin kasar.

A cewar kakakin hukumar, Femi Babafemi, sama da kunshin haramtattu kwayoyi 100 ake zargin wani mutum dan shekaru 52 ya shigo da su kasar, wanda ya dawo daga birnin Sao Paulo na kasar Brazil, bayan yada zango a Doha, a jirgin saman Qatar Airways.

Kakakin na NDLEA ya ce, an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar, bayan ya sauka a filin jirgin saman Legas, daga bisani aka gano kunshin haramtattun kwayoyin guda 101, wanda nauyinsu ya kai kilogram 13.2, an gano kwayoyin ne bayan an bincika jakar kayansa.

Babafemi ya ce, a tambayoyin farko da aka yiwa wanda ake zargin ya amsa cewa, an yi masa alkawarin biyansa kudi kimanin Naira miliyan 5 idan ya yi nasarar fasa-kwaurin haramtattun kwayoyin zuwa Lagas. (Ahmad)