logo

HAUSA

Xi ya jaddada muhimmin irran kasar Sin wajen tabbatar da wadatar abinci

2022-04-11 15:30:44 CMG Hausa

Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmin rawar da irran kasar Sin ke takawa wajen tabbatar da wadatar abinci a kasar.

Xi Jinping ya bayyana yayin da yake rangadi a wani dakin gwajin tsirrai dake birnin Sanya na lardin Hainan dake kudancin kasar cewa, kiyaye albarkatun tsirrai a cikin gida, ita ce hanya daya tilo ta tabbatar da wadatar abinci a kasar.

Ya ce domin tabbatar da albarkatun irrai sun kasance masu inganci da aminci, dole kasar ta kasance mai tsayawa da kafarta a fannin fasahar irrai.

Da yake bayyana muhimmancin ayyukan da suka shafi hakan, ya yi kira da a daukaka ruhin tsoffin masana kimiyya da masu bincike, ciki har da Yuan Longping.

Ya kuma yi kira da a ci gaba da zage damtse wajen raya masana’antar irrai ta kasar. (Fa’iza Mustapha)