logo

HAUSA

Xi yana rangadin aiki a birnin Sanya na lardin Hainan

2022-04-11 13:41:17 CMG Hausa

Da yammacin jiya Lahadi, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya ziyarci dakin gwajin irin hatsi na Yazhouwan da aka kafa a watan Mayun shekarar 2021, da cibiyar nazarin halittun teku ta birnin Sanya ta jami’ar teku ta kasar Sin dake birnin Sanya na lardin Hainan na kasar Sin, domin kara fahimtarsa kan yadda ake goyon bayan kirkire-kirkire a lardin, da kuma yadda ake kokarin raya kimiyya da fasahar teku a lardin.

Hakika a ko da yaushe, babban sakatare Xi yana mai da hankali matuka kan aikin nazarin teku. (Jamila)