logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da wani sabon shirin bunkasa lafiyar mata da yara

2022-04-11 10:21:56 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta gabatar da wani shirin da za a aiwatar, wanda ke da nufin mayar da hankali kan wasu muhimman ayyukan bunkasa lafiyar mata da yara, da take son cimmawa zuwa shekarar 2030.

Bisa shirin, zuwa 2030, cikin adadin yara 1,000, matsakaicin yawan likitocinsu zai karu zuwa 1.12, gadaje kuma zai kai 3.17 a asibitoci.

Har ila yau, shirin na sa ran adadin matan da za a yi wa binciken cutar kansar bakin mahaifa zai zarce kaso 70, yayin da na yaduwar cutar kanjamau daga uwa zuwa danta, zai ragu zuwa kasa da kaso 2 cikin dari.

Domin cimma wadannan muradu, shirin ya yi kira da a dauki dabarun da za su mayar da hankali kan jama’a da hada hannu wajen shigar da matakan kandagarkin cututtuka cikin ayyukan kiwon lafiya da kuma amfana daga likitancin gargajiya na Sin da likitancin yammcin duniya.

Bugu da kari, daga cikin manufofin shirin, akwai rage mace-mace mata yayin haihuwa da na jarirai, da fadada aikin binciken lafiya kafin aure da kafin haihuwa da inganta gangamin alluran rigakafi domin bunkasa garkuwar jikin yara. (Fa’iza Mustapha)