logo

HAUSA

Peter Kagwanja:Cudanyar Sin da Afirka na haifar da ci gaba

2022-04-11 10:38:29 CMG Hausa

Babban shugaban cibiyar nazarin tsare-tsaren manufofi ta nahiyar Afirka Peter Kagwanja, ya ce tattaunawa da hadin kai tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, sun haifar da ci gaba mai tarin yawa tsakanin al’ummun sassan biyu.

Masanin ya ce, a wannan karni na 21, Sin da Afirka sun amince su yi aiki tare cikin dogon lokaci. Kaza lika sassan biyu sun rungumi hadin gwiwa mai nagarta, da goyon bayan juna, domin ingiza nasarorinsu, yayin da ake fuskantar kalubale daban daban a tsarin gudanarwar harkokin kasa da kasa.

Mr. Kagwanja ya kara da cewa, alakar Sin da Afirka na da nasaba da dogon tarihin musayarsu. Tun daga lokacin fir’aunonin Masar Sinawa kan bi jiragen ruwa domin yin kasuwanci da sassan Afirka, kana masanan nahiyar su ma sun jima suna ziyartar kasar Sin.

Ya ce bayan tsawon lokaci na mamaya, da danniya, da wawashe yankunan su, sassan biyu sun sake daidaita tafiyar su, tare da kafa hanyar siliki a matsayin sabuwar kofar cudanya da musaya, musamman a wannan gaba da duniya ke kara dunkulewa wuri guda.  (Saminu)