logo

HAUSA

Sin ta kalubalanci babban sakataren NATO da ya dakatar da yada jita-jita game da matsayin Sin kan batun Ukraine

2022-04-11 20:39:28 CMG Hausa

Game da zargin da babban sakataren kungiyar tsaron NATO ya yi kan matsayin Sin game da batun rikicin Rasha da Ukraine, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya mayar da martani yayin taron manema labaru da aka gudanar a yau, inda ya yi kira ga kungiyar tsaron NATO, da ta hanzarta dakatar da yada jita-jita da ma takala kan kasar Sin, ta kuma daina yada kalamai na tayar da hargitsi da nuna kiyayya. Ya ce, kungiyar tsaron NATO ta riga ta kawo rikici a nahiyar Turai, bai kamata ta kawo matsala ga zaman lafiyar nahiyar Asiya, da ma duniya baki daya ba.

Rahotanni na cewa, yayin da ake gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar tsaron NATO daga ranar 6 zuwa 7 ga wannan wata, babban sakataren kungiyar Jens Stoltenberg, ya zargi kasar Sin ta ki yin Allah wadai da yakin da Rasha ta tayar a kasar Ukraine. Zhao Lijian ya bayyana yayin da yake karin haske kan wannan batu cewa, shugabannin NATO, sun yi watsi da gaskiya, sun ci gaba yada jita-jita da zargi da nuna batanci ga kasar Sin da manufofin diplomasiyyarta na dogon lokaci, da yada ra’ayin Sin ta kawo barazana, kana nuna matsa lamba ga kasar Sin. Sin ta ki amincewa kuma tana adawa da neman tursasa mata, kuma ta sha gabatar da korafin ga kungiyar. (Zainab)