logo

HAUSA

Munanan hare-haren bindiga sun faru a sassan Amurka a karshen makon da ya gabata

2022-04-11 10:32:53 CMG Hausa

Munanan hare-haren bindiga sau da dama sun faru a sassa daban daban dake kasar Amurka a karshen makon da ya gabata, inda mutane sama da goma suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata.

Hukumar ‘yan sanda ta birnin Cedar Rapids a jihar Iowa ta kasar ta sanar da cewa, da asubahin jiya Lahadi, an ji karar bindiga a wata mashaya, bayan da ‘yan sanda suka isa wurin, sun tarar da cewa, mutane biyu sun rasa rayukansu, kana wasu goma sun jikkata, kuma kawo yanzu ba a cafke wani da hannu cikin harin ba.

Kana rahotannin da kafofin watsa labarai na Amurka suka gabatar sun nuna cewa, da sanyin safiyar jiya, an kai harin bindiga cikin taron jama’a a birnin Elgin na jihar Illinois, kuma a sanadin hakan, mutane shida sun jikkata, har ma wani daga cikinsu ya mutu.

A daidai wannan lokaci kuma, wasu ‘yan bindiga sun kai hari yayin wani taron jama’a a birnin Indianapolis dake jihar Indiana, inda mutum daya ya rasa ransa, saura biyar kuma suka jikkata.

Ban da haka kuma, hare-haren bindiga su ma sun karu a birnin Grantville na jihar Georgia, da birnin Memphis na jihar Tennessee, da birnin Houston na jihar Texas, da sauran sassan kasar ta Amurka a karshen makon da ya gabata, inda a kalla mutane uku suka rasa rayuka ko jikkata yayin hare-haren.

Alkaluman da shafin yanar gizo na “takardun hare-haren bindiga” na Amurka ya wallafa a ranar 10 ga wata sun nuna cewa, a kalla mutane 11,668 sun rasa rayukan su, kana wasu 9,270 sun jikkata, yayin hare-haren bindiga da aka aikata a kasar a bana, kuma munanan hare-haren bindiga, da suka hallaka mutane hudu ko sama da hudu ko jikkata mutane sun faru har sau 127. (Jamila)