logo

HAUSA

MDD: Bala’in fari zai iya jefa mutane miliyan 15 cikin garari a kusurwar Afrika

2022-04-10 17:02:39 CMG Hausa

 

Shiyyar kusurwar Afrika tana fuskantar matsanancin fari da ba ta taba ganin irinsa ba cikin gomman shekaru, inda aka yi kiyasin cewa, za a shafi mutane miliyan 15 daga kasashen Kenya, da Somalia da Habasha, ana kuma fargabar halin da ake ciki ta fuskar jin kai zai ci gaba da tabarbarewa, kamar yadda shafin intanet na MDD ya wallafa a kwanan baya.

An ruwaito cewa, mai yiwuwa ne matsalar karancin ruwan sama na wasu shekaru a jere, za ta haifar da munanan matsalolin jin kai a shiyyar, wacce dama ta jima tana fuskantar illolin matsalolin tashe-tashen hankula, da matsalar sauyin yanayi, da kwararar farin dango, da kuma cutar annobar numfashi ta COVID-19. Hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa ta yi gargadin cewa, akwai bukatar gaggawa ta samar da ba da tallafin jin kai yadda ya kamata, domin kaucewa fuskantar tabarbarewar yanayin ayyukan jin kai a duk shiyyar.

A cewar Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a ranar 8 ga wata, matsalar karancin abinci a Somalia ta yi matukar muni tun a farkon wannan shekarar da muke ciki. Hasashen karuwar yunwa na baya-bayan nan da aka gudanar, ya nuna cewa, ‘yan kasar Somalia sama da miliyan 6 za su iya fuskantar matsanancin karancin abinci tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin wannan shekara. Ya bayyana cewa, bala’in farin ya kara yin muni a wasu sassan kasar Somalia, wanda ya kasance mafi muni da Somalia ba ta taba fuskantar irinsa ba a cikin shekaru 40.(Ahmad)