logo

HAUSA

Firaministan Sin ya jaddada aniyar hadin gwiwa da kasashe masu magana da harshen Portugal

2022-04-10 21:13:26 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kiran a karfafa hadin gwiwa da kasashe masu magana da harshen Portugal.

Li ya yi wannan tsokaci ne a yayin da ya halarci bikin bude taron musamman na ministoci na dandalin hadin gwiwar raya tattalin arziki da ciniki na kasar Sin da kasashe masu magana da harshen Portugal (PSCs), wacce aka fi sani da Forum Macao.

Li ya kara da cewa, yawan ciniki a tsakanin kasar Sin da kasashe masu magana da harshen Portugal, ya zarce dalar Amurka biliyan 100 a shekaru biyar a jere, yayin da adadin ya kai dala biliyan 200 a shekarar da ta gabata, lamarin da ya nuna a fili irin gagarumin ci gaban da aka samu da kuma kyakkyawar makomar hadin gwiwar bangarorin biyu.

A cewar firaministan, kasar Sin za ta kara samar da gudunmawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar duniya da kara azama kan ci gaba da samun wadata a kasa da kasa, ta hanyar hada kai da kasashe masu magana da harshen Portugal har ma da duniya baki daya.

Li ya ce, kasar Sin a shirye take ta kara yin hadin gwiwa da kasashe masu magana da harshen Portugal a fannonin allurar riga-kafi, da magunguna, da kiwon lafiya, da kuma kafa cibiyar musaya wajen yaki da annoba a yankin musamman na Macao na kasar Sin.

Firaministan kasar Sin ya bukaci a kara yin ciniki da zuba jari cikin ‘yanci, ya ce, kasar Sin a shirye take ta kara inganta hadin gwiwarta wajen bunkasa kayayyakin more rayuwa, da masana’antu, da yin tsimin makamashi, da kare muhalli.

Mahalarta taron sun hada da wakilan gwamnatin Sin, da na kasashe masu magana da harshen Portugal takwas, da suka hada da Angola, da Brazil, da Cape Verde, da Guinea-Bissau, da Mozambique, da Portugal, da Sao Tome da Principe, da kuma Timor-Leste.(Ahmad)