logo

HAUSA

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Kan Al’adun Sin Da Afirka Karo Na Farko

2022-04-10 17:14:42 CMG Hausa

A jiya ne, aka gudanar da taron tattaunawa kan al’adun Sin da Afirka karo na farko mai taken “sa kaimi ga raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a sabon zamani ta hanyar mu’amalar al’adun juna”, wanda kwalejin ilmin zamantakewar al’umma ta Sin, da kwalejin nazarin Afirka na kasar Sin, da kuma ofishin kungiyar AU dake kasar Sin suka dauki nauyin shiryawa.

A wajen taron, babban sakataren kwalejin ilmin zamantakewar al’umma na kasar Sin Zhao Qi, ya yi nuni da cewa, an gudanar da taron tattaunawar cikin nasara, wanda ya kasance sabon dandalin yin mu’amalar al’adu a tsakanin Sin da Afirka wanda kwalejin nazarin Afirka na kasar Sin ta kafa, kana zai sa kaimi wajen zurfafa mu’amalar al’adu a tsakanin Sin da Afirka.

Zaunannen wakilin kungiyar AU dake kasar Sin Rahamtalla M. Osman ya yi jawabi da cewa, a halin yanzu, ana fuskantar matsaloli da dama a duniya, kasashe da yankuna suna fuskantar kalubale a fannin samun ci gaba, kana an samu bunkasuwar fasahohin sadarwa da yanar gizo, an kara maida hankali ga ikon yin magana kan al’adu. A halin yanzu, mu’amalar al’adu ta riga ta kasance muhimmiyar hanyar sa kaimi ga raya dan Adam, don haka gudanar da taron tattaunawa kan al’adun Sin da Afirka karo na farko ya dace da yanayin da ake ciki. Kwalejin nazarin Afirka na kasar Sin da kungiyar AU sun karbi bakuncin shirya taron tattaunawar, wanda ya dace da bukatun Sin da Afirka, kana zai sa kaimi ga masanan Sin da Afirka wajen kara yin hadin gwiwa da juna don ba da shawarwari game da yadda za a bunkasa kasashen Afirka.

Masana da wakilan matasa da ‘yan kasuwa da kuma jami’an diplomasiyya na kasashen Afirka dake kasar Sin da yawansu ya zarce 120 sun halarci taron tattaunawar. (Zainab)