logo

HAUSA

Bankin raya kasar Sin ya yi matukar taimakawa ci gaban makamashi mai tsafta a rubu’in farkon bana

2022-04-10 17:16:57 CMG Hausa

Bankin raya kasar Sin (CDB), ya ninka kudaden tallafawa ayyukan samar da makamashi mai tsafta a rubu’in farko na wannan shekarar da muke ciki.

A cewar bankin na CDB, ya fidda rancen kudi da yawansa ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 109, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 17.12, domin tallafawa ci gaban makamashi mai tsafta, da sauya fasalin samar da makamashin da aka saba amfani da su zuwa hanyar kaucewa gurbata muhalli.

A cikin rubu’in farko na wannan shekara, an samar da rancen kudi da ya kai jimillar yuan biliyan 76.5 domin gudanar da ayyukan bunkasa samar da makamashi mai tsafta da suka hada da makamashin nukiliya, da na iska, da makamashin solar mai amfani da hasken rana. (Ahmad)