logo

HAUSA

Iran ta sanya takunkumi kan Amurkawa 24 bisa zarginsu da keta doka

2022-04-10 16:36:00 CMG Hausa

 

Kasar Iran ta ayyana sanya takunkumi kan karin jami’ai da daidaikun mutane 24 na kasar Amurka bisa samunsu da laifukan dake shafar ayyukan ta’addanci da keta hakkokin bil Adama, kamar yadda shafin intanet na ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya wallafa a ranar 9 ga wata..

Wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta nuna cewa, mutanen sun taka rawa wajen taimakawa aikata ta’addanci, da yada ruhun ta’addanci, da kuma keta hakkokin bil Adama, ta kara da cewa, ta sanya mutanen cikin jerin sunayen wadanda ta kakabawa takunkumi, matakin da ya dace da dokokin kare hakkin dan Adam na Iran da dokokin yaki da ayyukan ta’addanci na kasar.

Ma’aikatar ta ci gaba da cewa, wadannan mutane sun kuma ba da gudunmawa wajen tallafawa, da shiryawa, da aiwatarwa, da kuma inganta tsauraran matakan da Amurka ta yi kan al’ummar kasar Iran, da gwamnatin kasar Iran, tare kuma da daukar nauyi da goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda da taimakawa ayyukan ta’addanci da taimakawa miyagun ayyukan da Isra’ila ke kaddamarwa a shiyyar, musamman ma keta hakkokin al’ummar Falastinawa.

Sanarwa ta kara da cewa, matakan kashin kai da Amurka ta dauka, sun kara lalata yanayin da al’ummar Iran ke ciki, musamman yayin da aka samu barkewar annobar COVID-19 inda kasar ta gaza samun damar samun magunguna da hidimomin kiwon lafiya da muhimman kayayyakin kiwon lafiya, sannan an tauye muhimman hakkokin kasar.

Wadannan matakai, a cewar ma’aikatar, sun yi matukar saba muhimman dokokin kasa da kasa kuma sun keta hakkin bil Adama a zahiri.(Ahmad)