logo

HAUSA

An bude taron ministocin kudi da gwamnonin manyan bankunan kasashe mambobin BRICS karo na 1 a shekarar 2022

2022-04-09 17:14:29 CMG Hausa

An gudanar da taron farko a bana, na ministocin kudi da gwamnonin manyan bankunan kasashe mambobin kungiyar BRICS ta kafar bidiyo, a jiya Jumma’a . Taron mai taken "Raya dangantakar abota mai inganci don kirkirar sabon zamanin ci gaban duniya", ya tattauna kan batutuwan da suka shafi yanayin tattalin arziki da daidaita manufofi, da sabon bankin raya kasa, da zuba jari kan ababen more rayuwa, da cibiyoyin binciken masana a fannin kudi na BRICS da dai sauransu. Kana an yi musayar ra'ayi kan sakamakon da ake sa ran samu daga hadin gwiwar hada-hadar kudi tsakanin kasashen BRICS a bana.

Ministan kudi na kasar Sin, Liu Kun ya bayyanawa taron cewa, a shekarar 2022, kasar Sin za ta ci gaba da hada hannu da bangarori daban daban don inganta hadin gwiwar hada-hadar kudi ta kasashen BRICS, tare da cimma daidaito, yana mai cewa hakan zai share fage sosai kan taron koli karo na 14 na BRICS a fannonin manufar kudi da sakamakon da za a samu.

Liu Kun ya kara da cewa, a halin yanzu, karfin ingantuwar tattalin arzikin duniya na raguwa, yanayin kasa da kasa kuma na da sarkakiya da tsanani, kuma ci gaban duniya ya gamu da cikas. Don haka, ya kamata kasashen BRICS su sauke nauyin dake wuyansu, da hada gwiwa, da karfafa daidaituwar manufofi bisa manyan tsare-tsare, da taimakawa farfadowar tattalin arziki mai dorewa, da nufin samun ci gaban duniya mai karfi, da kiyaye muhalli yadda ya kamata, da kuma gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam. (Mai fassara: Bilkisu)