logo

HAUSA

Li Keqiang ya nanata bukatar karfafa tattalin arzkin yayin da ake fuskantar karuwar kalubale

2022-04-09 17:03:38 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da a yi kokarin daidaita aikin shawo kan annobar COVID-19 da raya al’umma, yana mai cewa, yanayin duniya mai sarkakiya da sake bullar cutar a cikin gida, sun kara haifar da karuwar rashin tabbas da kalubale ga ci gaban tattalin arziki.

Li Keqiang, wanda kuma mamba ne na zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana haka ne lokacin da yake jagorantar wani taron karawa juna sani kan yanayin tattalin arziki, wanda ya samu halartar masana da ‘yan kasuwa.

Mahalarta taron sun gabatar da shawarwari kan manufofin raya tattalin arziki da inganta jigila da sufuri da tabbatar da samun amfanin gona da bunkasa kirkire kirkire a fannin kasuwanci.

A cewar firaministan, jigon ci gaba da raya tattalin arzikin kasar kan mizanin da ya dace ya dogara ne da inganta samar da ayyukan yi da daidaita matakan farashi.

Bugu da kari, ya ce wasu harkokin kasuwanci na fuskantar matsi, yana mai cewa ya kamata a dauki matakai domin taimakawa kananan kamfanoni, musammam domin su tsallake wahalhalu.

Bugu da kari, ya yi kira da a fadada bude kofa da daidaita cinikayya da jarin waje da kuma farashin musayar takardar kudi na Renminbi a matsayin ingantacciyar hanyar shawo kan rashin tabbas daga waje.