logo

HAUSA

Albarkatun kankara na taimakawa jama’ar Xinjiang samun wadata da farfado da karkara

2022-04-09 16:11:50 CMG Hausa

Daukar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing da na nakasassu na lokacin sanyi sun sa kaimi ga raya wasannin kankara a kasar Sin. Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin dake da albarkatun kankara, ita ma ta amfana a fannin.

A sakamakon wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing, jihar Xinjiang na ci gaba da fadada sana’ar yawon shakatawa na kankara a cikin 'yan shekarun nan, tare da mai da " albarkatun sanyi" na kankara zuwa "tattalin arziki mai karfi” dake inganta ci gaba mai inganci.

Yanzu, jihar Xinjiang tana amfani da damar ci gaban tattalin arziki a fannin kankara bayan lokacin wasannin Olympics na lokacin sanyi, da nufin inganta samun wadata da farfado da karkara. (Mai fassara: Bilkisu Xin)