logo

HAUSA

Rasha ta bayyana aniyarta na janyewa daga wakilcin mamba a hukumar kare hakkin dan adam ta MDD

2022-04-08 10:49:35 CMG HAUSA

 

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta bayyana aniyar kasar na kawo karshen zamanta mamba a hukumar kare hakkin dan adam ta MDD.

A sanarwa da ma’aikatar ta fitar tace, bangaren Rashan ya yi la’akari da kudirin da aka gabatar a babban taron MDD a ranar 7 ga watan Afrilu a New York na neman janye wakilcin kasar Rasha a hukumar kare hakkin dan adam ta MDD, inda kasar ta ayyana matakin da cewa ya saba doka kuma wani makirci ne irin na siyasa da aka bijiro da shi da nufin yin matsin lamba ga matsayin wakilcin kasar a MDD da mayar da kasar saniyar ware a harkokin diflomasiyya.

Sanarwar ta kara da cewa, a halin yanzu, wasu rukunin kasashe ne suke juya akalar kwamitin majalisar domin cimma muradun kashin kansu.

A cewar ma’aikatar harkokin wajen, kasar Rasha za ta ci gaba da bayar da gudunmawa wajen kare hakkin dan adam, duk da cewa ta dauki wannan matakin. (Ahmad)