logo

HAUSA

MPP: Tsohon shugaban Burkina Faso ba shi da cikakken 'yanci

2022-04-08 09:44:24 CMG HAUSA

 

Jam'iyyar MPP ta tsohon shugaban kasar Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore da aka ba shi izinin komawa gida a ranar Laraba, ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, tsohon shugaban ba shi da cikakken 'yanci.

A ranar Laraba ne, gwamnatin rikon kwarya ta kasar ta sanar da cewa, an baiwa Kabore izinin komawa gidansa da ke Ouagadougou, babban birnin kasar, yayin da za a dauki matakan tabbatar da tsaron lafiyarsa.

Sanarwar ta ce, jam’iyyar MPP ta yi maraba da wannan shawara, tare da nuna jin dadinta ga wadanda ke ciki da ma a wajen kasar, da suka yi gangamin ganin an sake shi.

Jam'iyyar MPP ta kuma yi kira ga gwamnatin rikon kwarya, da ta amince da bukatu daban-daban da aka gabatar mata, na sakin Kabore ba tare da gindaya wani sharadi ba. (Ibrahim)