logo

HAUSA

Shugaban IOC ya gabatar da wasikar godiya ga ma’aikatan sa kai na gasar Beijing 2022

2022-04-08 16:52:47 CMG HAUSA

 

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa (IOC) Thomas Bach, ya bayyana farin cikinsa da nuna godiya ga dukkan ma’aikatan sa kai wadanda suka ba da gudummawa a lokacin gasar wasannin Olympic da ajin nasakassu nata gasar Beijing 2022.

A wasikar da ya rubuta, Bach ya yabawa dukkan ma’aikatan sa kai da suka taka rawar gani a gasar wasannin motsa jiki ta Beijing 2022. Ya ce ma’aikatan sun cancanci yabo, idan aka yi la’akari da tarihin da Beijing ya kafa na zama birni na farko a duniya da ya karbi bakuncin dukkan gasanni, na lokacin zafi da na sanyi, shugaban na IOC ya ce, ma’aikatan sa kai wani muhimmin ginshiki ne wajen kafa wannan muhimmin tarihi.

Ya ce, “a madadin kwamitin Olympic, na gode muku, masoyana ’yan sa kai, saboda babbar gudunmawar da kuka bayar wajen samun nasarar gasannin Olympic da ajin nakassu na gasar Beijing 2022. Murmushinku ya faranta mana zuciya." (Ahmad Fagam)