logo

HAUSA

Matakan kasar Sin na dakile COVID-19 sun tabbatar da gudanar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing cikin aminci

2022-04-08 14:40:07 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a yau Juma’a cewa, ingantattun matakan kandagarki da dakile yaduwar COVID-19 da kasar Sin ta dauka, sun tabbatar da karbar bakunci da gudanar wasannin Olympics na lokacin hunturu da irinsa na nakasassu na 2022, da aka yi a Beijing, cikin aminci ba tare da wata tangarda ba.

Xi Jinping ya bayyana hakan ne yau, yayin wani taro don girmama wadanda suka bada muhimmiyar gudunmawa ga gudanar wasannin 2 na Olympics na Beijing na lokacin hunturu na 2022 cikin nasara.

A cewar shugaban, duk da mummunan tasirin COVID-19 da ake fuskanta a duniya, kasar Sin ta sanya kiwon lafiyar dukkan mahalarta gaba da komai, ta kuma dauki manufofin kare kwayar cutar daga sake shiga kasar domin kare sake barkewarta, da kuma tsaurara aiwatar da matakan kandagarki da dakile ta.

Ya kara da cewa, yayin da wasannin ke gudana, kaso 0.45 na jami’an dake kebabben wurin gudanar da wasannin ne gwaji ya nuna sun kamu da cutar. Kuma dukkansu sun samu ingantacciyar kulawa. Kana babu wani rukunin mutane da ya kamu da cutar, haka kuma ba a samu yaduwarta ba, inda aka tabbatar da babu cutar a birane.

Bugu da kari, Xi Jinping ya ce, manufofin kasar Sin na yaki da annobar, sun haifar da da mai ido, inda suka bayar da gudunmawa wajen gabatarwa duniya darussan yaki da annobar da kuma karbar bakuncin muhimman tarukan kasa da kasa.

Shugaba Xi Jinping ya ce, kamar yadda ’yan wasannin kasashen waje suka bayyana, idan akwai wata kasa da ta dace da samun lambar yabo ta fuskar yaki da annobar COVID-19, to kasar Sin ta cancanta. (Fa’iza Mustapha)