logo

HAUSA

Kasar Sin na adawa da amfani da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam wajen matsawa wasu kasashe lamba

2022-04-08 20:39:29 CMG Hausa

Dangane da matakin da babban taron MDD ya dauka, na dakatar da Rasha daga zama mamba a kwamitin kare hakkin bil Adama na MDD, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya jaddada matsayin kasarsa a taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau Jumma’a, inda ya jaddada cewa, kasar Sin tana adawa da siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam, da nuna adawa da yin zabe, da nuna kiyayya, kuma bisa amfani da ma’auni biyu kan batutuwan, kana da adawa da amfani da batutuwan hakkin dan Adam wajen matsa lamba ga sauran kasashe.

Yayin da yake amsa tambayar, Zhao ya yi nuni da cewa, “Ba a bayyana yadda aka tsara kudurin a fili ba, kuma ba a yi shawarwari da dukkan kasashe mambobin kwamitin kamar yadda aka saba, don sauraren ra'ayinsu sosai ba. Irin wannan matakin zai kara fadada rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashe mambobin, ta yadda za su kara samun sabani a tsakanin bangarori masu ruwa da tsaki, kana za a kara hura wutar rikici, kuma hakan ba zai yi amfani wajen kawar da rikici, balle ma taimakawa wajen inganta shawarwarin zaman lafiya ba. (Mai fassara: Bilkisu)