logo

HAUSA

Abin ban mamaki! Kirkirar fasahar CMG ta haskaka wasannin Olympics na lokacin hunturu!

2022-04-07 20:42:00 CMG Hausa

Kwanan baya, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya aike da wasika zuwa babban rukunin rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, inda ya nuna yabo da godiya ga nasarar da ya samu, wajen watsa shirye-shirye kai tsaye, yayin wasannin Olympics na lokacin hunturu da aka shirya a birnin Beijing, da kuma yadda yake yada wasannin Olympic na kasa da kasa yadda ya kamata.

A matsayinsa na gidan rediyo da talabijin na kasa mai masaukin baki, kuma abokin hadin kai na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa, a aikin watsa shirye-shirye kai tsaye ta kafar talabijin, CMG ya dogara da tsarin dabarun fasahar "5G+4K/8K+AI", tare da babbar fasahar watsa shirye-shirye ta 4K / 8K dake jagorantar duniya, da manyan na’urorin daukar bidiyo na fasaha da ya yi nazari da kansa, da kuma fitattun masu ba da tabbaci kan fasahar watsa shirye-shirye kai tsaye, don cimma makasudin “Wasannin Olympics na fasaha, da amfani da fasahar 8K don kallon wasannin Olympics”, kana ya karya ingantaccen matsayin bajintar sadarwa, na sama da mutane biliyan 62.814 da suka kalli wasannin Olympics na hunturu, ta hanyar amfani da dandamali daban daban na CMG. (Mai fassara: Bilkisu)