logo

HAUSA

Sin na maraba da manyan jam'iyyun Sudan ta Kudu, game da cimma matsaya da suka yi kan tsare-tsaren tsaron na lokacin mulkin wucin gadi

2022-04-07 21:23:39 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Alhamis cewa, a kwanan baya, manyan jam'iyyun kasar Sudan ta Kudu sun cimma matsaya daya, tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar tsare-tsaren tsaro na lokacin mulkin rikon kwarya, wanda wani muhimmin ci gaba ne a yunkurin samar da zaman lafiya a kasar, don haka kasar Sin ta yi maraba da hakan.

Baya ga haka, Zhao ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta yaba da rawar da Sudan da sauran kasashe makwabtan ta suka taka, da kuma wanda hukumomin kasa da kasa da na shiyya-shiyya suka yi, wajen sa kaimi ga cimma yarjejeniyar, tana mai fatan bangarori masu ruwa da tsaki a Sudan ta Kudu, za su aiwatar da abubuwan dake cikin yarjejeniyar, da inganta yunkurin mika mulki a kasar, da nufin tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar cikin dogon lokaci.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)