logo

HAUSA

Yawan RMB a asusun ajiyar waje na duniya yana karuwa akai-akai

2022-04-07 16:59:58 CMG Hausa

Bisa labarin da aka bayar a shafin intanet na RT, an ce, bisa binciken da asusun IMF ya yi a kwanan nan, ya nuna cewa, a rubu’i na hudu na shekarar 2021, jimilar RMB a asusun ajiyar waje na duniya ta kai RMB Yuan biliyan 336.1, wadda ta kai kashi 2.79 cikin dari na kudaden asusun ajiyar waje na duniya baki daya.

Labarin ya bayyana cewa, bisa kiddidigar “kudaden dake cikin asusu ajiyar waje na hukumar ”, yawan RMB ya karu kadan bisa rubu’i na uku na shekarar 2021 wato kashi 2.66 cikin dari. Ya zuwa karshen shekarar 2021, yawan RMB ya kai matsayi na biyar a cikin “kudaden dake cikin asusun ajiyar waje na hukumar. ”

Labarin ya nuna cewa, masana na asusun IMF suna tsammanin dalilan karuwar RMB su ne babban ci gaban tattalin arzikin Sin da kuma yanayi na yin amfani da kudin Sin RMB a karin wurare daban daban na duniya. Sun kara da cewa, a cikin yanayin da Rasha da kasashen yamma suke kakkaba wa juna takunkumai da kuma rikicin tattalin arzikin duniya, yawan RMB zai karu cikin karin sauri a bana.

Labarin ya kuma bayyana cewa, kiddidiga ta nuna cewa, sama da rabin kudaden ajiya dake cikin hannun babban bankin galibin kasashen duniya shi ne dalar Amurka. Duk da haka, tasirin dala a duniya yana raguwa a kai a kai. A shekarar 2007, kusan kashi 70 cikin dari na kudaden ajiya na babban bankin galibin kasashen duniya shi ne dalar Amurka, amma a cikin rubu’i na hudu na bara, adadin ya ragu zuwa kashi 58.8 cikin dari. (Mai Fassarawa: Safiya Ma)