logo

HAUSA

Xi zai halarci bikin karrama wadanda suka taka rawar gani a gasar wasannin Olympics da ajin nakasassu ta lokacin hunturu ta Beijing

2022-04-07 09:30:07 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai halarci wani taro da za a gudanar a babban dakin taron jama'a da ke birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a safiyar gobe Jumma’a, domin karrama wadanda suka ba da gagarumar gudummawa, a gasar wasannin Olympics da ta ajin nakasassu na lokacin sanyi na shekarar 2022 da suka gudana a birnin Beijing, tare da gabatar da jawabi. (Ibrahim)