logo

HAUSA

Rasha ta fitar da takardu masu alaka da ayyukan kwayoyin halittu na sojan Amurka a duniya

2022-04-07 10:42:20 CMG HAUSA

 

A ranar 6 ga wata agogon wurin, karkashin laimar kasar Rasha, kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da wani taro, kan batutuwan da suka shafi kare muhallin halittu. A yayin taron, kasar Rasha ta fitar da wasu takardu masu alaka da ayyukan kwayoyin halittu na sojan da Amurka ke gudanarwa a kasar Ukraine da ma duniya baki daya, inda ta zargi kasar Amurka da karya “yarjejeniyar hana makaman kare dangi iri na kwayoyin halittu”, da haifar da barazana ga zaman lafiya da tsaron kasashen duniya.

Takardun da kasar Rasha ta fitar a yayin taron sun nuna cewa, kasar Amurka ta tallafawa dakunan gwaje-gwajen kwayoyin halittu na fararen hula da na soji kimanin 336 a kasashe 30 dake sassan duniya, wadanda suke warwatse a kasashen Afirka, da Turai, da Asiya da sauransu. (Ibrahim)