logo

HAUSA

Sakataren MDD ya yi maraba da labarin agajin abinci da ya isa yankin Tigray na Habasha

2022-04-07 09:28:46 CMG HAUSA

 

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi maraba da samun labarin cewa, manyan motocin da ke dauke da kayayyakin abinci da man fetur, sun isa yankunan Tigray da Afar na kasar Habasha, bayan ayyana tsagaita bude wuta.

A cikin wata sanarwar da babban jami'in na MDD ya fitar, ya yi kira ga dukkan bangarori, da su ci gaba da yin aiki tukuru tare da bibiyar alkawurran da suka dauka na saukaka isar da agajin jin kai ga dukkan mabukata.

Guterres ya sake nanata kiran da ya yi na dawo da ayyukan gwamnati a yankin Tigray, da suka hada da na banki, da wutar lantarki da sadarwa, da kuma hanyoyin kasuwanci.

Sanarwar ta ce, MDD ta nanata kudurinta na ba da goyon baya ga tabbatar da zaman lafiya da kyakkyawar makoma ga daukacin ’yan kasar Habasha. (Ibrahim)