logo

HAUSA

Sin ta harba sabon tauraron dan adam mai binciken sararin samaniya

2022-04-07 11:13:11 CMG HAUSA

 

A yau Alhamis kasar Sin ta harba sabon tauraron dan adam mai binciken sararin samaniya daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Tauraron, samfurin Gaofen-3 03, wadda aka harba da na’urar daukar tauraron dan adam ta Long March-4C, da misalin karfe 8 da saura minti 13 na safe agogon Beijing, kuma a yanzu haka ya kama hanyar zuwa sararin samaniyar cikin nasara.

Aikin harba tauraron dan adam din shi ne karo na 414 a jerin ayyukan harba tauraron dan adam da na’urar roka ta Long March. (Ahmad)