logo

HAUSA

Wang Yi ya taya sabon ministan wajen Mauritania murnar kama aiki

2022-04-07 21:00:05 CMG Hausa

Mamban majalissar gudanarwa, kuma ministan wajen kasar Sin Wang Yi, ya aike da sakon taya Mohamed Salem Ould Merzoug murnar kama aiki, a matsayin ministan wajen kasar Mauritania.

Cikin sakon da ya aike ga Merzoug a jiya Laraba, Wang ya bayyana aniyarsa ta aiki tare da ministan wajen na Mauritania, domin bunkasa musaya, da hadin gwiwa tsakanin ma’aikatun wajen kasashen biyu, tare da habaka tsare tsare a harkokin kasa da kasa da na shiyyoyi, ta yadda hakan zai ingiza ci gaban dangantaka tsakanin Sin da Mauritania. (Saminu)