logo

HAUSA

Wang Chen ya tattauna da mataimakin shugaban majalisar dokokin Niger

2022-04-07 09:31:59 CMG HAUSA

 

Wang Chen, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, kuma mataimakin shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, ya tattauna ta kafar bidiyo da mataimaki na 1, na shugaban majalisar dokokin kasar jamhuriyar Niger, Kalla Ankourao.

Yayin tattaunawar ta jiya, Wang Chen ya ce, Sin da Niger sahihan aminai ne kuma muhimman abokan hulda. Ya ce a shirye majalisar wakilan jama’ar kasar Sin take, ta hada hannu da majalisar dokokin Niger, wajen zurfafa musaya da koyi da juna, da taka muhimmiyar rawa wajen inganta hadin gwiwa ta fuskar tsara dokoki da kuma gina Ziri Daya da Hanya Daya tare. Har ila yau, ya ce za su hada hannu wajen karfafa yaki da annobar COVID-19 da inganta ginin al’ummomin Sin da Afrika mai makoma ta bai daya a sabon zamani. Ya kuma godewa Niger bisa taimakon da take ba Sin a batutuwan da suka shafi Taiwan da Hong Kong da Xinjiang da kuma batutuwan kare hakkokin jama’a.

A nasa bangaren, Kalla Ankourao ya ce, Niger tana tare da kasar Sin, yana mai godewa muhimmin taimakon da kasar Sin take ba kasarsa a bangarori da dama. Ya ce a shirye majalisar dokokin Niger take, ta zurfafa musaya da takwararta ta kasar Sin da kuma bada gudunmmawa ga raya huldar kasashen biyu da ma ta Sin da Afrika. (Fa’iza Mustapha)