logo

HAUSA

Za a kammala ginin majalisar dokokin Zimbabwe da kasar Sin ta samar da kudin gina ta

2022-04-06 09:41:26 CMG Hausa

Ministan kananan hukumomi da ayyukan gwamnati na kasar Zimbabwe July Moyo, ya bayyana cewa, ana gab da kammala aikin sabon ginin majalisar dokokin kasar da ke tsaunin Hampden, mai tazarar kilomita 25 daga arewa maso yammacin Harare, babban birnin kasar, wanda gwamnatin kasar Sin ta samar da kudaden aikin, inda dan kwangilar dake kula aikin ya kai mataki na karshe na aikin.

Ministan ya shaida wa manema labarai cewa, yanzu haka kamfanin Shanghai Construction Group dake gudanar da wannan aiki, yana kokarin kammala bayan ginin, yayin da tuni aka kammala sanya kujeru da tebura da sauran kayayyaki a cikin ginin majalisar.

Magatakardar majalisar Kennedy Chokuda ya bayyana cewa, tuni aka sanar da majalisar cewa, sabon gidan nata ya kusa kammala.

An dai fara aikin gina sabon ginin majalisar ce a shekarar 2018. Gwamnatin kasar Sin tana gina sabon ginin majalisar mai hawa shida ne a matsayin kyauta ga kasar Zimbabwe.

Ginin mai kujeru 650, zai maye gurbin majalisar ta yanzu mai kujeru 100 wadda aka gina tun lokacin Turawan mulkin mallaka, wanda ya kasa wajen gudanar da harkokin majalisar dokoki, kuma ba zai iya daukar 'yan majalisa da ma'aikata 350 ba. (Ibrahim)