logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a kai zuciya nesa game da abun da ya auku a Bucha

2022-04-06 20:30:42 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce kasar sa na fatan dukkanin sassan masu ruwa da tsaki za su kai zuciya nesa, su kuma kaucewa furta zarge zarge marasa tushe, kafin a kai ga kammala cikakken bincike game da abun da ya auku a garin Bucha na kasar Ukraine.

Zhao Lijian, wanda ya bayyana hakan a Larabar nan, yayin zantawa da manema labarai, ya ce Sin na mai da hankali a kan halin jin kai a Ukraine, da ma halin matsuwa da fararen hular kasar ke ciki.

Jami’in ya kara da cewa, bai dace a siyasantar da batun jin kai ba, kuma ya kamata duk wani mataki da za a dauka, ya dogara kan dalilai na gaskiya.

Ya ce Sin na goyon bayan dukkanin shawarwari, da matakai da za a iya aiwatarwa, domin saukaka halin jin kai a Ukraine, za ta kuma yi aiki tare da sauran sassan kasa da kasa, wajen tabbatar da kare rayukan fararen hula.

Wasu rahotanni sun ce, an gano gawawwakin a kalla mutane 280, ciki har da kananan yara a garin na Bucha, wanda ke wajen birnin Kiev. Tuni dai ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta musanta zargin da Ukraine ta yi mata, na kisan fararen hula a Bucha.   (Saminu)