logo

HAUSA

Ministocin wajen Sin Canada sun tattauna ta wayar tarho

2022-04-06 10:03:41 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da takwararsa ta kasar Canada Melanie Joly, jiya Talata bisa bukatar da ta gabatar.

Wang ya bayyana cewa, a kullum kasar Sin tana kallo tare da daidaita dangantakar dake tsakaninta da Canada bisa manyan tsare-tsare da kuma dogon lokaci. Yana mai cewa, halin da ake ciki a halin yanzu bai dace da muradun kasashen biyu ba. Don haka, ya yi kira ga kasar Canada, da ta tinkari matsalolin, tare da yin hadin gwiwa da kasar Sin. Wang ya kuma gabatar da shawarwari guda uku dangane da hakan.

Na farko, ya kamata Canada ta yiwa kasar Sin kallo na basirar bil hakki da gaskiya, gami da hakikanin manufofin ta.

Na biyu, ya kamata kasashen biyu su mutunta muhimman muradun juna, su kuma daina haifar da abubuwan da za su kawo cikas ga ci gaban dangantakar dake tsakaninsu.

Na uku, ya kamata Canada ta martaba 'yancin kanta, kana ta magance tsoma baki na babu gaira babu dalili daga ketare.

Wang Yi ya ce, kasar Sin na fatan kasar Canada, za ta yi aiki tare da kasar Sin wajen kawar da tsoma baki daga waje, ta shawo kan matsaloli, da tabbatar da samun bunkasuwa mai dorewa, da kwanciyar hankali a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Bangarorin biyu sun kuma yi musayar ra'ayi kan batun rikicin kasar Ukraine.

Ya kuma sanar da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi cikakken bayani kan matsayin kasar Sin game da wannan batu. Yana mai cewa, kasar Sin tana kira ga dukkan bangarorin da wannan batu ya shafa, da su yi tunani cikin natsuwa da hankali, da samar da damammaki na zaman lafiya da bude kofa ga yin shawarwari. (Ibrahim Yaya)