logo

HAUSA

Sabbin takunkuman EU kan Rasha zai shafi makamashi, a cewar ministan Faransa

2022-04-06 10:13:48 CMG Hausa

Bruno Le Maire, ministan kudi da tattalin arzikin kasar Faransa ya ce, za a shigar da makamashi cikin jerin sabbin takunkuman da kungiyar tarayyar Turai za ta kakabawa kasar Rasha.

A cewar mataimakin shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Turai, kana kwamishinan kasuwanci, Valdis Dombrovskis, ana kammala tsare-tsare game da batun sanya sabon takunkumin.

Ya ce, baya ga fannin makamashin, za kuma a takaita harkokin shigi da ficin kasuwanci da ake gudanarwa da Rasha, kuma akwai karin daidaikun mutane da ’yan kasuwar kasar da batun takunkumin karo na biyar zai shafa.

A cewar Le Maire, za a dauki wasu matakai na gajeren zango domin baiwa magidantan kasashen EU kariya, da ’yan kasuwa, daga tsadar farashin makamashin da za su iya fuskanta. Wasu daga mambobin kasashe kamar Sifaniya da Faransa, tuni sun riga sun dauki matakan daidaita farashin albarkatun man fetur.

Ya ce, a shirin dogon zango kuwa, kungiyar na bukatar gina tattalin arzikinta mai cin gashin kai domin samar da albarkatun da ake bukata a cikin gida, don tabbatar da fannin makamashin yana cin gashin kansa, kuma yana aiki bisa tsarin da ba ya gurbata muhalli. (Ahmad Fagam)