logo

HAUSA

An bukaci shugabannin Somaliya su rungumi tsarin maslaha don kammala zaben kasar

2022-04-06 10:49:42 CMG Hausa

Bangarorin kasa da kasa dake hulda da kasar Somaliya, sun bukaci shugabannin kasar, da su rungumi tsarin tattaunawa da yin maslaha a matakin karshe don kammala shirye-shiryen babban zaben kasar.

Abokan huldar da suka hada da kungiyar tarayyar Afrika, da tarayyar Turai, da MDD da sauran kasashen yamma, sun bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwa a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya cewa, sun samu kwarin gwiwa, kasancewar a yanzu haka sama da kashi 91 bisa 100 na kujerun majalisar wakilan kasar an riga an zabe su. Don haka suna ganin lokaci ya yi da ya kamata a kammala zabar raguwar kujerun nan ba da jimawa ba.

Kawo yanzu, jahohi biyu ne kadai suka rage, jahar Hirshabelle da Jubaland, wadanda ba a kammala zabar mambobin majalisar wakilan kasar ba.

Ana sa ran ’yan majalisar dattijan kasar 54 da na wakila 275, za su yi hadin gwiwa don zabar sabon shugaban kasa nan gaba cikin wannan shekarar ta 2022. (Ahmad)