logo

HAUSA

Iran ta ce sabbin takunkuman da aka kakkaba mata yayin da ake tattaunawa a Vienna na nuna mugin nufin Amurka

2022-04-06 11:23:32 CMG Hausa

Kakakin gwamnatin kasar Iran ya bayyana cewa, sabbin takunkuman da Amurka ta kakkaba mata a daidai lokacin da ake gudanar da tattaunawa ba tare da wata rufa-rufa ba a Vienna, a kokarin da ake na farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma a shekarar 2015, ya nuna mugin nufin Washington da rashin daukar tattaunawar da muhimmanci.

A watan Yulin shekarar 2015 ne, kasar Iran ta sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar kasar wato (JCPOA) a takaice, tare da manyan kasashen duniya. Sai dai kuma, tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya janye Amurkar daga yarjejeniyar a watan Mayu 2018.

Daga watan Afrilun 2021 zuwa yanzu, an gudanar da zagayen tattaunawa da dama a babban birnin kasar Austriya, tsakanin Iran da sauran bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar ta JCPOA, wato kasashen Sin, da Rasha, da Birtaniya, da Faransa da kuma Jamus, domin farfado da yarjejeniyar.

Iran dai ta dage kan samun tabbacin cewa, gwamnatin Amurka mai ci, ba ta sake yin watsi da yarjejeniyar ba, inda ta yi kira da a dage takunkuman da aka kakkaba mata ta hanyar da ta dace. (Ibrahim)