logo

HAUSA

Kasar Sin tana son a kawo karshen tashin hankali da gaggauta daidaita rikicin Ukraine

2022-04-06 10:38:13 CMG Hausa

Wakilin kasar Sin ya ce, kasar tana matukar bukatar a dakatar da tashin hankali, kana a kawo karshen yakin Ukraine ba tare da bata lokaci ba.

Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a kwamitin sulhun MDD, ya bayyana cewa, dakatar da tashin hankali da kawo karshen rikicin Ukraine cikin gaggawa shi ne abin da al’ummar kasa da kasa ke bukata, kuma shi ne babban abin da kasar Sin ke son ganin ya tabbata.

Zhang ya ce, Rasha da Ukraine sun shiga zagaye daban-daban na tattaunawar sulhu, kuma kasar Sin tana maraba da bangarorin biyu da su rungumi tafarkin tattaunawar sulhu, su kawo karshen wahalhalun da ake fuskanta, da bambance-bambance, kana su ci gaba da gina cikakkun matakan da za su tabbatar da warware rikicin.

Babban sakataren MDD ya yi tsokaci kan batun. Sannan mataimakiyarsa a fannin siyasa da gina zaman lafiya, Rosemary DiCarlo, ita ma ta gabatar da jawabi kai tsaye ga kwamitin sulhun, yayin da mataimakin babban sakataren a sashen kula da ayyukan jinkai, Martin Griffiths, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Shi ma shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya gabatar da jawabinsa ta kafar bidiyo. (Ahmad)