logo

HAUSA

MINUSMA na bincike game da rahoton kisan fararen hula a Mali

2022-04-05 15:27:10 CMG

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD mai aiki a Mali ko MINUSMA a takaice, ta ce tana aiki tare da mahukuntan Mali, domin tantance gaskiyar abun da ya faru, yayin da dakarun gwamnatin kasar, suka yi arangama da wasu mayaka da ake zaton na da alaka da kungiyar IS ko Al-Qaida cikin makon jiya, lamarin da ya sabbaba kisan fararen hula masu tarin yawa.

Akwai dai rashin tabbas game da adadin rayukan da aka rasa yayin bata-kashin, ko da yake alkaluma na nuna wadanda aka kashe din sun haura mutum dari.

Da yake karin haske game da al’amarin, mataimakin kakakin babban magatakardar MDD Farhan Haq ya ce “Jami’an wanzar da zaman lafiya da abokan aikin mu, sun yi matukar damuwa da samun rahoton kisan fararen hula, suna kuma aiki tukuru wajen tabbatar da hakikanin abun da ya faru, ciki har da tantance ko an keta hakkokin bil adama yayin tashin hankalin da ya auku”.

Haq wanda ya shaidawa manema labarai hakan a jiya Litinin, yayin taron ‘yan jarida da aka saba gudanarwa, ya ce tawagar bincike za ta ziyarci wurin da aka fafata, wanda ke da nisan kilomita kusan 400, daga arewa maso gabashin birnin Bamako fadar mulkin kasar.   (Saminu)