logo

HAUSA

Shanghai: An yiwa sama da mutane miliyan 24 gwajin cutar COVID-19 a rana guda

2022-04-05 16:26:11 CMG Hausa

A jiya Litinin, mahukuntan birnin Shanghai suka bayyana cewa, an kammala karbar samfurin gwajin cutar COVID-19 daga al’ummar birnin su sama da miliyan 24, a wani mataki na dakile bazuwar annobar, wadda ta sake bulla a sassan birnin.

Wata sanarwa da aka fitar ta nuna cewa, an sanya birnin Shanghai cikin matakin kulle na wucin gadi, bayan da adadin masu harbuwa da cutar ta COVID-19 ya karu matuka a ‘yan kwanakin baya bayan nan.

Kaza lika, sanarwar ta ce a yanzu haka mahukuntan birnin na ci gaba da ayyukan gwaji, da killace masu dauke da cutar, tare da bincike da tantance yanayin bazuwar ta. Za kuma a ci gaba da aiwatar da wadannan matakai bisa tsari.

Jami’an lafiya sama da 38,000 daga larduna da yankunan kasar Sin 15 ne suka isa Shanghai, domin aikin dakile cutar ta COVID-19, a cewar hukumar kiwon lafiyar kasar Sin NHC.

Da safiyar Talatar nan, mahukuntan birnin sun ce a jiya Litinin, an tabbatar da harbuwar mutane 268 da cutar, an kuma gano mutane 13,086 dauke da ita ba tare da sun nuna alama ba.  (Saminu)