logo

HAUSA

Ghana ta kaddamar da wani shirin jan hankalin masu yawon bude ido daga fadin duniya

2022-04-05 17:03:39 CMG Hausa

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya kaddamar da wani shirin kasa da kasa, da zummar jan hankalin masu yawon bude ido zuwa kasar dake yammacin Afrika, yayin da gwamnatinsa ke neman karfafa kudin shigar bangaren.

Akufo Addo, ya kaddamar da shirin “Destination Ghana” a birnin London na Birtaniya, wanda shi ne na farko cikin jerin shirye-shiryen dake da nufin gayyata da maraba da masu yawon bude ido daga fadin duniya, zuwa Ghana.

Kamar sauran kasashen duniya, Ghana dake yammacin Afrika ta fuskanci mummunan tasirin annobar COVID-19 kan bangaren yawon bude ido, bisa la’akari da yadda cutar ta kawo tsaiko ga tafiye-tafiye a duniya, a kokarin dakile yaduwarta. Sai dai, Akufo-Addo na ganin akwai damarmaki tattare da yawon bude ido don shakatawa da ganin halittu.

Shugaban ya kuma bayyana kyakkyawan yanayin siyasa da kasar ke ciki a matsayin jigo na jan hankalin karin masu yawon bude ido daga kasashen waje.

A cewarsa, kasarsa tana gudanar da shirye-shiryen kyautata bangaren, inda yanzu haka ake yi wa wuraren yawon shakatawa na kasar gyaran fuska. (Fa’iza Mustapha)