logo

HAUSA

Kasar Sin bata neman cimma wani muradi a siyasar duniya daga batun Ukraine

2022-04-05 17:02:33 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce Kasar Sin ba ta neman cimma wani muradi na son kai a siyasar duniya dangane da batun Ukraine, haka kuma, ba ta nuna halin ko-in-kula, bare kuma ta nemi kara rura wutar rikicin.

Wang Yi ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Ukraine Dmytro Kuleba. Wadda ita ce zantawa ta biyu da suka yi ta wayar tarho, bayan ta ranar 1 ga watan Maris, tun bayan barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine.

A cewar Wang Yi, ainihin abun da Sin take sa rai game da yanayin Ukraine shi ne zaman lafiya. Kuma Sin na maraba da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine din, yana mai kira ga bangarorin biyu su tsaya ga yin tattauanwa, ba tare da la’akari da kalubalen da suke fuskanta da kuma bambancin dake tsakaninsu ba.

Wang Yi ya kuma jaddada muhimmancin daukar darasi daga rikicin da kuma lalubo hanyoyin wanzar da zaman lafiya mai dorewa a Turai. Ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin, da su hau teburin sulhu tare da samar da ingantaccen tsarin tabbatar da tsaro mai dorewa a Turai, bisa daidaito, kuma dunkulalle.

Bugu da kari, ya ce kasar Sin ta dauki matsayi na hakika ba tare da son kai ba, kuma za ta ci gaba da taka rawar gani bisa nata tsari. Kana ta yi ammana Ukraine na da basirar daukar zabin da ya dace da muradun jama’a.

A nasa bangaren, Dmytro Kuleba, ya ce Sin babbar kasa ce, inda ya kira ta da karfin dake ingiza zaman lafiya. Ya ce Ukraine ta shiryawa ci gaba da tuntubar kasar Sin, kuma tana fatan Sin din, za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen rikicin.

Ya kuma amince da matsayar kasar Sin kan batun na Ukraine, inda ya bayyana godiyarsa ga taimakon jin kai da ta samarwa kasarsa. (Fa’iza Mustapha)