logo

HAUSA

Antonio Guterres ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kan sa don gane da kisan fararen hula a Bucha

2022-04-05 15:44:53 CMG

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kan sa, don gane da zargin kisan daruruwan fararen hula a yankin Bucha, dake wajen birnin Kyiv na kasar Ukraine.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafin sa na Tiwita, Guterres ya ce "Na yi matukar kaduwa, da jin labarin kisan fararen hula a Bucha. Abu ne mai matukar muhimmanci a gudanar da bincike mai zaman kan sa, wanda zai fayyace komai a fili".

Magajin garin Bucha Anatoly Fedoruk, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, a kalla mutane 280, ciki har da kananan yara aka gano gawawwakin su a Bucha, bayan da sojojin Rasha suka mamaye yankin, ko da yake daga bisani dakarun sojin Ukraine sun kwace iko da yankin, mai nisan kilomita 28 daga arewa maso yammacin Kyiv.

A jiya Litinin, shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukrainen, ya ziyarci yankin, inda ya bayyana kisan fararen hular da ya auku, a matsayin laifin yaki. To sai dai kuma Rasha ta musanta zargin aikata kisan kiyashin, tana mai cewa, hotunan bogi ne aka yi amfani da su a matsayin gawawwaki.

Alkaluman baya bayan nan da hukumar kare hakkin bil adama ta MDD ta fitar, sun nuna cewa, adadin fararen hula da aka hallaka a Ukraine sun kai 3,455. MDD ta yi kira da a tsagaita wuta, tana mai alkawarta yin duk mai yiwuwa, wajen tallafawa fararen hula su sake farfadowa.  (Saminu)