logo

HAUSA

Ana bikin ranar Qingming a kasar Sin

2022-04-05 16:38:45 CMG Hausa

Yau Talata 5 ga watan Afrilu, ita ce ranar Qingming, ko kuma ranar share kaburburan magabata a kasar Sin, inda al’ummar kasar su kan tuna da mamata gami da ‘yan mazan jiya. Wannan rana, na kunshe da al’adun gargajiya masu dimbin tarihi na wurare daban-daban a kasar, wadanda har yanzu ake rayawa.

A ranar, rundunonin sojojin kasar Sin su kan shirya bukukuwa kala-kala don tunawa da jarumai ‘yan mazan jiya. Kana, mutanen kasar Sin suna gudanar da bukukuwan share kaburburan ‘yan mazan jiyan da suka sadaukar da ransu ga kasar, don nuna alhini da girmamawa gare su. (Murtala Zhang)