logo

HAUSA

Sama da ‘yan ci rani 90 suka nutse a tekun Meditireniya

2022-04-04 16:51:21 CMG Hausa

Kamfanin dillancin labarai na AP, ya rawaito cewa, wasu ‘yan ci rani sama da 90 sun nutse a tekun Meditireniya, bayan da wani kwalekwale da suke ciki ya yi hatsari, a kan hanyar su ta zuwa Turai daga arewacin Afirka. AP ya ce ‘yan ci ranin sun bar kasar Libya ne cikin makon jiya, ko da yake ba a iya tantance a wace rana ne suka yi hadarin ba.

A shekarun baya bayan nan, masu fataucin mutane na amfani da matsalolin siyasar Libya, wajen yin fasakwaurin mutane zuwa Turai, ta kan iyakokin kasar mai makwaftaka da kasashe 6. Ana yawan dibar ‘yan ci ranin ne cikin jiragen ruwa marasa inganci, a kuma ratsa teku cikin yanayi mai matukar hadari.

A cewar hukumar dake lura da ‘yan gudun hijira ta duniya IOM, kusan ‘yan ci rani 300 ne suka rasu, ko aka bayyana bacewarsu, a kan hanyar su ta tekun na meditireniya, tsakanin ranar 1 ga watan Janairu zuwa 28 ga watan Maris din da ya wuce. Kana an cafke wasu 3,100 a kan hanyar su, aka kuma mayar da su Libya.

IOM ta ce, a shekarar 2021 da ta gabata ma, an cafke wasu ‘yan ci ranin a kalla 32,425, aka kuma mayar da su Libya. An kuma ayyana wasu mutanen 1,553 matsayin wadanda suka nutse a tekun, duka dai a shekarar ta bara.    (Saminu)