logo

HAUSA

Al-Burhan ya bukaci tawagar MDD da ta kasance a tsaka-tsaki kan rikicin siyasar kasar

2022-04-04 16:56:14 CMG Hausa

Shugaban majalisar rikon kwarya na kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, ya yi kira ga tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Sudan (UNITAMS) da ta nesanta kanta daga dukkan bangarorin kasar, a daidai gabar da ake fama da rikicin siyasa a kasar.

Kalaman nasa na zuwa ne, yayin wata ganawa da shugaban tawagar ta UNITAMS Volker Perthes, a Khartoum, babban birnin kasar, inda Al-Burhan ya nuna shakku kan yadda tawagar ta UNITAMS ta yiwa kwamitin sulhu na MDD karin haske na baya-bayan nan, game da halin da ake ciki a kasar, kamar yadda majalisar ta bayyana cikin wata sanarwa.

An dai ruwaito Al-Burhan na cewa, tattaunawar ba ta shafi dukkan al'amura a kasar ba, kuma ba ta hada da ci gaba masu kyau da aka samu a kasar ba.

A nasa bangare kuwa Perthes ya ce, bayanin nasa ya ta’allaka ne da bayanai da rahotannin da ofishinsa dake birnin Khartoum ya shirya, a cewar sanarwar. 

Wakilin na MDD ya bayyana cewa, a shirye yake ya sake nazartar duk wasu bayanai marasa inganci dake kunshe cikin rahoton da aka mika wa MDD.

Taron dai ya zo ne kwana guda, bayan da Al-Burhan ya yi gargadin cewa, idan tawagar ta MDD ta wuce gona da iri kan nauyin da aka dora mata, ko kuma ta tsoma baki a harkokin cikin gidan Sudan, to za a iya korar Perthes.

A jawabin da ya yiwa kwamitin sulhun na MDD a makon da ya gabata dai, Perthes ya yi gargadin cewa, tabarbarewar tattalin arziki, da yanayin jin kai da kuma tsaro a Sudan, sun faru ne saboda rashin tsayayyiyar gwamnati a kasar tun watan Oktobar 2021, da kuma yadda ake murkushe masu zanga-zangar neman mulkin farar hula.(Ibrahim)