logo

HAUSA

Iran: Amurka ba ta damu da kasashen musulmi ba

2022-04-04 16:27:44 CMG Hausa

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, ya ce ko kadan Amurka ba ta damu da halin da kasashen musulmi ke ciki ba, maimakon haka, burin ta shi ne cimma muradun kashin kai da tabbatar da danniya.

Shugaba Raisi ya bayyana hakan ne, yayin zantawarsa ta wayar tarho da takwaransa na Iraqi Barham Salih a jiya Lahadi. Ya ce kasarsa ta tallafawa Iraqi, a fannin wanzar da hadin kan kasa, da samun ‘yancin kai, da tsaro, da tabbatar da gurbin ta a matakan kasa da kasa da na shiyya, kuma tsaron Iraqi na da matukar tasiri ga tsaron shiyyar su baki daya.

Ya ce "Alakar ‘yan uwantaka da abokantaka tsakanin Iran da Iraqi, ta wuce batun makwaftaka kadai".

A nasa bangare kuwa, shugaban Iraqi cewa ya yi, akwai bukatar inganta hadin gwiwar kasashen biyu, domin shawo kan kalubalolin dake addabar yankin, musamman bisa la’akari da manyan bukatun samar da daidaito da tsaron yankin.

Shugaba Barham Salih ya kara da cewa, ana iya shawo kan tashe tashen hankula da shiyyar ke fuskanta, ta hanyar hada karfi da karfi tsakanin kasashen dake ciki, ba tare da bukatar tsoma bakin kasashen waje ba.   (Saminu)