logo

HAUSA

Sin: Dubban likitoci ne suka garzaya Shanghai don taimaka mata yaki da COVID-19

2022-04-04 16:04:53 cri

Rahotanni daga kasar Sin na cewa, kimanin likitoci 10,000 a duk fadin kasar ne, suka garzaya zuwa Shanghai, cibiyar kasuwanci ta kasar, domin taimakawa cibiyar wajen dakile yaduwar annobar COVID-19.

Jiya Lahadi, dubun dubatan likitoci ne, suka isa birnin Shanghai mai yawan jama'a miliyan 25 ta cikin jiragen kasa masu saurin tafiya, wadanda suka taso daga yankunan Tianjin da Hubei da Shandong da Jiangxi.

Hukumar lafiya ta birnin Shanghai ta bayyana cewa, tun da farko akwai tawagogin likitocin da suka fito daga lardunan Zhejiang da Jiangsu da Anhui da ke kusa, da suka riga suka isa birnin domin shiga aikin yaki da annobar.

A ranar Asabar din da ta gabata, mahukuntan birnin Shanghai sun ba da rahoton mutane 438 da aka tabbatar sun kamu da cutar ta COVID-19 a cikin gida, da kuma mutane 7,788 da suka kamu da cutar ba tare da nuna alamu ba. (Ibrahim)