logo

HAUSA

Wadanne Matakai Kasar Sin Ta Dauka Don Tabbatar Da Tsaro A Cikin Gidanta?

2022-04-04 19:49:12 CMG Hausa

Harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wani jirgin kasan fasinjoji a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, babban birnin Najeriya a kwanaki baya, ya girgiza al’ummar duniya sosai. Lamarin da ya fusata ‘yan kasar, inda wasu abokaina ke ta tattauna matakan da suka dace a dauka don dakile ayyukan ‘yan fashi a Najeriya. A ganina, watakila za a iya duba wasu matakan da kasar Sin ta taba dauka don tabbatar da tsaro a cikin gidanta.

Kamfanin ba da shawara na kasar Amurka Gallup ya gabatar da wani rahoto dangane da ayyukan shari’a na kasashe daban daban a shekarar 2020, inda ya sanya kasar Sin a matsayi na 3 cikin wasu kasashe da yankuna 144 ta fannin ingancin harkokin shari’a. Abun da ya nuna cewa, kasar Sin na cikin kasashen da suka fi samun kwanciyar hankali da tsaro a cikin gida a duniya. Sai dai idan mun waiwayi tsakanin kimanin shekarar 1980 ta 2000, za mu ga cewa yanayin tsaro na kasar Sin bai kai na yanzu ba. A lokacin, ana samun ayyukan ‘yan fashin da suke tare hanya, da barayin da suke satan abubuwa sosai a kasar Sin. Sai dai ta yaya kasar Sin ta yi nasarar daidaita wannan matsala daga bisani?

Akwai dalilai na kai tsaye guda biyu. Na farko shi ne, a dinga dakile masu aikata laifuka da inganta ayyukan tabbtar da tsaro. Daga shekarar 1983 zuwa ta 2001, jami’an tsaron kasar Sin sun gudanar da manyan ayyukan dakile masu aikata munanan laifuka a kusan ko wace shekara, inda a cikin shekaru 3 na farko kadai, ‘yan sandan kasar suka gurfanar da gungun masu aikata laifuka kimanin dubu 197 a gaban kuliya. Sa’an nan hukumomin tsaron kasar, sun yi kokarin kafa tsarin sa ido na kyamarori don tabbatar da tsaro, da inganta fasahohin binciken laifukan da aka aikata. Zuwa shekarar 2021 ‘yan sandan kasar Sin sun cimma nasarar kama kashi 99.8% na mutanen da suka aikata laifin kisa. Ban da wannan kuma, yadda aka haramta mallakar bindiga shi ma ya taka muhimmiyar rawa a fannin tabbatar da tsaro a kasar ta Sin.

Dalili na biyu da ya sa aka yi nasarar daidaita yanayin tsaro a kasar Sin, shi ne ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma mai dorewa. Sanin kowa ne, talauci da rashin adalci wasu manyan dalilai guda 2 ne da suke haddasa aikata laifuka. Saboda haka, gwamnatin kasar Sin ta yi matukar kokarin raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama’a. Yanzu haka, cikin biranen kasar Sin, hukumomi na kokarin gyara wasu ungwanni marasa ci gaba, don samar da sabbin gidaje masu kyau ga mutane marasa karfi. Kana a cikin yankunan karkara, an yi nasarar fid da dukkan manoma daga kangin talauci. Ban da haka kuma, an yi kokarin raya bangaren ilimi, ta yadda aka yi nasarar koya wa karin mutane fasahohin aiki, da ilimi game da dokoki. Duk wadannan abubuwa sun taimaka sosai wajen rage aikata laifi.

Sa’an nan, baya ga wadannan matakan da kasar Sin ta dauka, akwai wani dalili na tushe da yake tabbtar da tsaro a cikin gidan kasar Sin, wanda ya kasance babbar manufar mulki ta jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, dake rike da ragamar mulki a kasar, wato “mai da moriyar jama’a a gaban kome”. A kokarin ganin an kare rayukan jama’a, duk da mawuyacin halin da ake fuskanta a fannin tattalin arziki sakamakon annobar COVID-19, hukumomin kasar Sin na ci gaba da kokarin killace da kulawa da duk wani mutum da ya kamu da cutar COVID-19. Don tabbatar da moriyar jama’a, a yayin da kasar Sin ke rungumar tsarin ciniki na baiwa kasuwa damar yin halinta, tana ci gaba da ba da dimbin tallafi ga mutane marasa karfi don magance komawarsu cikin wani yanayi na fama da talauci. Wannan dalili shi ma ya sa mahukuntan kasar Sin ke daukar duk wani matakin da ya shafi tsaro, tattalin arziki, ko kuma zaman al’umma, don hana abkuwar aikata laifi daga tushe.

Duk da wadannan bayanai da na zayyana, ina fatan ganin mahukuntan Najeriya sun dauki matakin da ya cancanta, wanda ya dace da yanayin da kasar ke ciki, ta yadda ita ma za ta yi nasarar tabbatar da tsaro a cikin gida. A watan Ramadan mai tsarki da muke ciki, muna rokon Allah Ubangiji da ya ba mu tsaro da kwaciyar hankali a kasashenmu da ma duniya baki daya. Amin. (Bello Wang)