logo

HAUSA

Shugaban kasar Pakistan ya rushe majalissar dokoki bayan watsi da kudirin yanke kauna ga gwamnatin firaminista Imran Khan

2022-04-04 17:08:43 CMG Hausa

Shugaban kasar Pakistan Arif Alvi, ya rushe majalissar dokokin kasarsa a jiya Lahadi, bisa shawarar firaministan kasar Imran Khan, bayan da kudurin yanke kauna ga gwamnatin kasar mai ci ya gamu da cikas.

Majalissar dokokin ta tsara kada kuri'ar yanke kauna ga gwamnatin da firaminista Imran Khan ke jagoranta ne da safiyar Lahadi, amma kafin a kai ga hakan, sai ministan watsa labaran kasar Fawad Chaudhry, ya bayyana matakin a matsayin haramtacce karkashin kundin mulkin kasar, yana mai cewa, yunkurin ‘yan majalissar na sauya gwamnati bisa bukatar wata gwamnatin waje, dake samun goyon bayan ‘yan adawa a cikin kasar, juyin mulki ne ta hanyar fakewa da kuri’ar yanke kauna.

A ranar 27 ga watan Maris, yayin da yake jawabi gaban dandazon al’ummar kasar a birnin Islamabad, Firaminista Khan ya ce, ya samu wata wasika a ranar 7 ga watan na Maris, kwana guda kafin gabatar da waccan bukata ta kada kuri’ar yanke kauna a zauren majalissar dokokin, daga wani jakadan Pakistan dake wata babbar kasa, inda a cikin wasikar aka sanar da jakadan waccan bukata, tare da jan kunnen mahukuntan kasar game da abun da ka iya biyo baya, idan har ba a tsige firaminista Khan ba.

Daga bisani Mr. Khan ya bayyana cewa, Amurka ba ta ji dadin ziyarar da ya kai kasar Rasha cikin watan Fabarairu ba, inda ta bayyanawa jami’an Pakistan a hukumance, bukatar sauya gwamnatin da yake jagoranta, ta hanyar jefa kuri’ar yanke kauna.   (Saminu)