logo

HAUSA

Al’ummar musulmi a Xinjiang sun fara azumin watan Ramadan

2022-04-04 16:36:28 CMG Hausa

Tun daga jiya Lahadi 3 ga watan nan, al’ummar musulmi a birnin Urumqi na jihar Xinjiang ta kasar Sin sun fara ibadar azumin watan Ramadan na bana.

A cibiyar birnin Urumqi, akwai wani babban masallaci da ake kira White Mosque, mai tarihin kusan shekaru 100, inda musulmai su kan taru don yin salloli, da karatun Alkur’ani mai tsarki, da gudanar da sauran wasu ibadu.

A babbar kasuwar kasa da kasa mai suna Xinjiang International Grand Bazaar dake Urumqi, ana sayar da abubuwa masu sigar musamman ta wurin.

A gaban shagunan sayar da kayan kade-kade, masu shagunan kan buga wasu kayan kidan gargajiya mai suna Dombra, don jawo hankalin masu yawon bude ido a wannan lokaci.

Da misalin karfe 10 da minti 20 na dare bisa agogon Beijing, musulmi za su yi bude baki a Xinjiang, inda su kan ci wainar Nang, da ‘ya’yan itatuwa daban-daban, a lokacin na bude baki a gidajen su.

Ana sa ran a ranar 3 ga watan Mayu, jama’ar musulmi a Xinjiang za su gudanar da shagulgulan karamar sallah. (Murtala Zhang)