logo

HAUSA

Jami’in Najeriya: Ana kokarin ceto fasinjojin jirgin kasan da suka bace

2022-04-03 16:24:20 CMG Hausa

Hukumar kula da sufurin jiragen kasan Najeriya NRC tana yin aiki tukuru tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin tabbatar da ganin an kubutar da fasinjojin jirgin kasan akalla 21 wadanda suka bace bayan harin da ‘yan bindiga suka kaddamar kan jirgin a daren Litinin, kamar yadda wani jami’in hukumar ya bayyana.

A sanarwar da manajan daraktan hukumar ta NRC, Fidet Okhiria, ya fitar a ranar Asabar, ya tabbatar da lafiyar kusan 170 daga cikin fasinjojin jirgin kasan.

Yace, hukumar tana yin hadin gwiwa da hukumomin tsaro wadanda tuni suka dukufa wajen yin dukkan abinda ya dace domin kubutar da fasinjojin da suka bace.

A daren Litinin din da ta gabata, jirgin kasan dake jigilar al’umma zuwa jahar Kaduna daga Abuja, babban birnin kasar, ya gamu da harin ‘yan bindiga a daidai garin Rijana, dake jahar Kaduna. A kalla fasinjoji takwas ne aka kashe a harin da kuma raunata wasu 26, kamar yadda gwamnatin jahar Kaduna ta sanar.

Bayanan da hukumar kula da sufurin jiragen kasan Najeriyar ta fitar ya nuna cewa, an tabbatar da fasinjoji 362 ne suka yanki tikitin hawa jirgin, kamar yadda gwamnatin Kadunan ta tabbatar.

A ranar Talata, hukumar NRC ta sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen kasan tsakanin Abuja zuwa Kaduna na wucin gadi, sakamakon halin rashin tabbas tun bayan faruwar harin.

Okhiria ya sanar cewa, hukumar kula da sufurin tana kokarin daidaita al’amurra domin dawo da harkokin sufurin ba tare da daukar dogon lokaci ba.

Game da tsaron lafiya, shugaban hukumar ta NRC yace, an yi wasu tanade-tanade domin tsaurara matakan tsaro a hanyar jirgin kasan domin kaucewa sake faruwar makamancin lamarin.(Ahmad)